6 Oktoba 2020 - 12:22
An Sallami Masu Ikirarin Jihadi Sama Da 100 A Mali

Rahotanni daga Mali, na cewa an sallami wasu mayaka dake ikirari da sunan jihadi su sama da dari da ake tsare dasu a kasar.

ABNA24 : An dai sallami fursunonin ne a yankin Niono dake tsakiyar kasar da kuma yankin Tessalit dake arewacin kasar.

Wannan dai an cikin tattaunawar da ake ta ganin an sallami wani babban jami’i a kasar da kuma wata ma’aikaciyar agaji ‘yar asalin kasar faransa da mayakan ke garkuwa dasu.

Wata majiya data bukaci a sakaya sunanta ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa wannan na daga cikin shirin da ake na neman ganin an sallami madugun ‘yan adawa na kasar Soumaïla Cissé da kuma ‘yar agajin nan ta kasar faransa, Sophie Pétronin.

342/